Trump Ya Yi Wa Sarkin Saudiyyah Bayani Kan Harin Da Ya Kai Wa Syria

Trump Ya Yi Wa Sarkin Saudiyyah Bayani Kan Harin Da Ya Kai Wa Syria

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz bayani kan yadda Amurka ta kaddamar da hari kan kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tuntubi sarkin Saudiyyah ta wayar tarho a jiya, inda suka tattauna batun harin da Amurka ta kaddamar a kan Syria bisa hujjar zargin yin amfani da makamai masu guba, sarkin na Saudiyya ya sanya wa Donald Trump albarka kan hakan.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jinjina wa Trump kan wannan hari, inda ya ce ya kamata a ci gaba da kai hare-hare domin kawo karshen gwamnatin Assad wadda Isra'ila ke kallonta  amatsayin barazana.

A zaman da mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya suka gudanar jiya  a kan wanann batu, Rasha ta bayyana harin da cewa ya sabawa dukkanin ka'idoji da dokoki na kasa, tare da tambayar Amurka da Birtaniya gami da Faransa cewa, idan har suna da gaskiya a kan zargin gwamnatin da su yi, me yasa suke jin tsoro a gudanar da bincike kan lamarin.

Wasu daga cikin majiyoyin diflomasiyya na cewa, gwamnatin Saudiyya ta biya kudin dukkanin makamai masu linzami guda 59 da Amurka ta harba a kan kasar Syria, kafin harba makaman.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky