Teheran Ta Yi Tir Da Kalaman Pompeo Kan Ofisoshin Jakadancinta

Teheran Ta Yi Tir Da Kalaman Pompeo Kan Ofisoshin Jakadancinta

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi tir da allawadai da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya firta kan ofisohin jakadancin, wanda ya zarga da hannu a shirye shiryen ayyyukan ta'addanci.

Da yake bayyana hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Qassemi, ya ce kalamman na Pompeo, abun dariya ne, don kuwa basu da tushe balle makama, wanda kuma a cewarsa kamfe ne na Amurka kamar kulun na nuna kiyaya da kuma bata wa Jamhuriya Musulinci ta Iran suna.

Mista Qassemi, ya ce tarihi dai ya nuna misalai dayewa na tsoma baki da shishigi da leken asiri da ta'addanci da hadassa fitina da Amurka ke yi a cikin kasashen duniya da dama, wanda hakan kuma ya sabawa huldar diflomatsiyya.

Ya kara da cewa har koda yaushe, ofisohin jakadancin Iran, a sauren kasashen na aiki kafada da kafada da kasashen da take alaka dasu don ci gaba, wanda kuma manufar Amurka shi ne ganin ta ruguza wannan alaka ta tsakanin Iran da abokanta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky