Tarayyar Turai Zata Kakabawa Duk Kamfanin Kungiyar Ta Ta Daina Hulda Da Iran Takunkumi.

Tarayyar Turai Zata Kakabawa Duk Kamfanin Kungiyar Ta Ta Daina Hulda Da Iran Takunkumi.

Tarayyar turai ta bada sanarwan cewa zata kakabawa duk kamfanin kasashen tarayyar wanda ya dakatar da huldar kasuwanci da Iran don biyayya ga Amurka, takunkumi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Nathalie Tocci mai magana da yawun jami'a mai kula da harkokin waje na tarayyar ta Turai, Federica Mogherini ya na fadar haka a ranar litinin, a hirar da ta hada shi da BBC Channel 4. 

A darin litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ta sake maida takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa iran kan shirinta na makamshin nukliya bayan da fice daga yerjejeniyar a cikin watan Mayun da ya gabata.

Federica Mogherini, tare da ministocin harkokin wajen kasashen Britania, Jamus da Faransa duk sun yi allawadai da maida wadannan takunkuman, kuma sun dauki makakan ganin kasar Iran ta amfani da yerjejeniyar ta shekara 2015, sannan takunkuman Amurka ba su yi wani tasiri a kan kasar ta Iran ba.

Daga cikin matakan da tarayyar ta zata dauka sun hada hara da dora takunki,i kan duk wani kamfanin kasashen kungiyar da ya dakatar da hulda da Iran sanadiyan biyayya ga takunkuman Amurka, wadanda basa bisa ka'ida.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky