Sojojin Siriya Sun Dakile Harin Da Aka Kai Wasu Filayen Jiragen Sama 2 Da Makamai Masu Linzami

 Sojojin Siriya Sun Dakile Harin Da Aka Kai Wasu Filayen Jiragen Sama 2 Da Makamai Masu Linzami

Sojojin kasar Siriya sun sami nasarar dakile wasu hare-hare da makamai masu linzami da aka kai sansanin sojojin saman kasar na Shayrat da ke lardin Homs da kuma filin jirgin saman soji na Dumair da ke birnin Damaskus a daren jiya Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Siriya SANA ya ba da rahoton cewa sojojin Siriyan sun sami nasarar kakkabo dukkanin makamai masu linzami guda 10 da aka harbo su tun kafin su kai ga gacinsu a sansanin sojin saman na Shayrat.

Har ila yau tashar talabijin din Al-Mayadeen da ke watsa shirye-shiryenta daga kasar Labanon ta ba da rahoton cewa sojojin Siriyan sun sami nasarar tarwatsa wasu makamai masu linzami guda uku da aka harbo su kan filin jirgin saman soji na Dumair da ke arewa maso gabashin birnin Damaskus, babban birnin kasar Siriya.

Amurka dai, ta bakin kakakin Ma'aikatar tsaron kasar, Pentagon, Eric Pahond, ta ce ba ita ta kai harin ba, kamar yadda haramtacciyar kasar Isra'ila, wacce ake zargi da kai harin ta yi gum da bakinta kan hakan duk kuwa da kokarin da kamfanin dillanin labaran Reuters ya ce yayi wajen jin ta bakin kakakin sojinta.

Harin dai yana zuwa ne 'yan kwanaki bayan da Amurka, Faransa da Birtaniyya suka kai wasu hare-hare da makamai masu linzami cikin Siriyan duk da nasarar da sojojin Siriyan suka samu na kakkabo sama da kashi 70% na makamai masu linzamin da suka harbo din da aka ce sun dara guda 100.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky