Sojojin Saudiyya Na Ci Gaba Da Kai Hari A Birnin Awamiyya

Sojojin Saudiyya Na Ci Gaba Da Kai Hari A Birnin Awamiyya

Jami'an tsaron Saudiyya sun sake aikewa da kayan yaki zuwa garin Awamiyya tare da tsananta hare-hare akan fararen hular da su ke cikinsa

Sojojin sun sake aikewa da kayan yaki zuwa garin Awamiyya tare da tsananta hare-hare akan fararen hular da su ke cikinsa.

Kamfanin dillancin labarun 'Tasnim" ya ambaci cewa a jiya laraba sojojin kasar ta Saudiyya sun yi amfani da motocin buldoza wajen rushe gidajen mutane a tsohuwar unguwar al-musawwarah mai tarihi.

Shedun ganin ido sun ce; sojojin na Saudiyya sun jefa gurneti a cikin unguwar al-dairah, haka nan kuma sun harba manyan bindigogi.

Sojojin na Saudiyya suna tilasta wa mazauna birnin ficewa daga gidajensu, sannan su rushe su.

Gwamnatin Saudiyya tana son korar 'yan shi'a daga garin na Awamiyyah da sauran garuruwan gabacin kasar da nan ne matsuguninsu kaka da kakanni, gabanin kafa kasar da ake kira Saudiyya.

Yankin gabacin gasar dai na 'yan shi'a su ke ne mafi yawancin man fetur din Saudiyya yake.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky