Sojojin Najeriya Sun Kashe Akalla Yan Bindiga 20 A Fafatawan Da Suke Da Su A Zamfara

Sojojin Najeriya Sun Kashe Akalla Yan Bindiga 20 A Fafatawan Da Suke Da Su A Zamfara

Akalla yan bindiga 20 suka mutu a lokacinda sojojin Nigeriya suka kai wa yan bindiga sumame a wurare daban daban a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto kakakin sojojin Kanar Mohammad Dole yana cewa a ci gaba da farmakin sharan Daji da sojojin kasar suka fara a jihar zamfara sun sami nasarar kashe yan ta'adda 20 sannan wasu kuma suka tsere daga raunuka a kananan hukumomin Tsafe da  Zurmi.

Mohammad Dole yace sojojin sun yi kwanton bauna wa yan ta'addan a wani wuri da ake kira Dansadau inda suka saba bi a lokacinda suke kai hare hare kan mutane a kauyukan yankin. Ya ce sun kashe  20 daga cikinsu wasu sun tsira da raunuka sannan sun kona babura da dama.

Kakakin sojojin ya kara da cewa a cikin wadanda sojojin suka halaka sun hada da Bello Dankobo da Sani Maza wadanda suka shahara da kekashewar zuciya a hare haren da suke kaiwa mutanen yankin.

Mohammad Dole ya kammala da cewa aikin sojojin ya dawo da zaman lafiya a wadannan yankuna.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky