Sojojin Lebanon Sun Dakatar Da Bude Wuta Don Sasantawa Kan Sojojin Da Ke Hannun Daesh

Sojojin Lebanon Sun Dakatar Da Bude Wuta Don Sasantawa Kan Sojojin Da Ke Hannun Daesh

Sojojin kasar Lebanon sun dakatar da bude wuta da mayakan kungiyar Daesh a Lebanon don tattauna batun sakin sojojin kasar da ke hannun Daesh.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Lebanon na cewa tun an fara tattaunawa don ganin sun sako sojojin kasar da suke tsare da su tun da dadewa a kan iyaka da kasar Syria.

Majiyar ta kara da cewa an dakatar da bude wutan da misalin karfe 7 na safen ranar Lahadi  agogon Lebanon. Har'ila yau wasu labarai sun bayyana cewa sojojin kasar Syria da na kungiyar Hizbullah sun tsagaita bude wuta a yankin kalamun na kasar ta Syria don fara tattaunawa kan sakin sojojin kasar wanda kungiyar Daesh take rike da su.

Kimamin mako guda kenan da sojojin kasar ta lebanon suka fara yakin kwatar yankunan kasar da ke hannun kungiyar Daesh da ke kusa da kan iyaka da kasar Syria.

A watan da ya gabata ne dakarun kungiyar Hizbullah suka kore yan ta'adda ta jibhatun nusra a yankin ersal na kasar lebanon.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky