Sojojin Jamhuriyar Niger Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Boko Haram Masu Yawa

Sojojin Jamhuriyar Niger Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Boko Haram Masu Yawa

Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Niger ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar halaka mayakan kungiyar Boko Haram akalla 10 a yankin kudu maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya habarta cewa: Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Niger a cikin daren jiya Asabar ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan sansanin sojin Niger da ke yankin jihar Diffa a shiyar kudu maso gabashin kasar, inda sojojin gwamnatin Niger suka maida martani kan gungun 'yan ta'addan tare da kashe akalla 10 daga cikinsu.

Har ila yau dauki ba dadi tsakanin bangarorin biyu ya yi sanadiyyar mutuwar sojan Niger guda tare da jikkatan wasu biyu na daban. Jihar Diffa tana kusa da kan iyaka ce da Tarayyar Nigeriya, kuma yankin arewa maso gabashin kasar ta Nigeriya shi ne yankin da yafi fama da matsalolin kungiyar Boko Haram.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky