Sojojin Iraki Suna Ci Gaba Da Murkushe 'Yan Kungiyar Da'ish A Arewacin Kasar

Sojojin Iraki Suna Ci Gaba Da Murkushe 'Yan Kungiyar Da'ish A Arewacin Kasar

Rundunar sojin Iraki ta sanar da cewa: Sojojin kasar sun fara murkushe mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish da suke gefen garin Tala'afar da ke lardin Nainawa a shiyar arewacin kasar ta Iraki.

Kwamandan rundunar sojin Iraki da ke jagorantar yantar da garin Tala'afar Abdul-Amir Rashid Yarullahi ya sanar da cewa: Kasar Iraki ba zata taba zama lafiya ba matukar sojojin kasar ba su tsarkake dukkanin kasar daga samuwar 'yan ta'adda ba. Yana mai fayyace cewa: Sojojin Iraki sun fara samun nasarar yantar da kauyuka da suke karkashin ikon 'yan kungiyar Da'ish a garin na Tala'afar. Kamar yadda dakarun sa-kai na Hashadus-Sha'abi suka kaddamar da hare-hare kan sansanonin mayakan kungiyar Da'ish tare da halaka wani adadi masu yawa na 'yan ta'addan.

A ranar Lahadin da ta gabata ce fira ministan kasar Iraki Haidar Abadi ya bada umurnin fara kaddamar da harin soji kan garin Tala'afar karshen tungar 'yan ta'adda a Iraki, bayan tsarkake garin Mosel daga mamayar 'yan ta'addan na kungiyar Da'ish. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky