Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kame Palastinawa 15

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kame Palastinawa 15

Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki a yankuna daban-daban na yammacin kogin jordan inda su ka yi awon gaba da palasdinawa 15

Tashar talabijin din al-alam ta ba da labarin cewa a yau talata, sojojin na Sahayoniya sun kai farmaki zuwa garuruwan qalqiliya, Ramallah, Kudus, da al-khalil da suke a yammacin kogin Jordan.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Sojojin na Sahayoniya sun kuma jikkata wasu paladinawa 19 a lokacin Zanga-zangar da suke yi ta kare hakkin komawa gidajensu na gado.

Wani jami'in kungiyar 'yanto Palasdinu Mahir Mazhar ya bayyana cewa; Sai idan an dauke takunkumin da aka kakabawa yankin na Gaza ne, palasdinawa za su dakatar da Zanga-zangar da suke yi domin tabbatar da hakkinsu na komawa gidajensu na gado da a ka kore su daga ciki, yayin kirkirar haramtacciyar kasar Isra'ila.

Tun a 2006 ne aka killace yankin na Gaza ta sama da ruwa da kasa, abin da ya mayar da yankin zama wani kurkuku.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky