Shugaban Siriya Ya Gode Wa Jagora Da Al'ummar Iran Saboda Goyon Bayansu

Shugaban Siriya Ya Gode Wa Jagora Da Al'ummar Iran Saboda Goyon Bayansu

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya bayyana godiyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sauran al'ummar Iran saboda irin goyon bayan da suke ba wa gwamnatinsa a fadar da take yi da ta'addanci.

Shugaba Asad din ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa Jagora Ayatullah Khamenei biyo bayan nasarar da sojojin kasar Siriyan suka samu na kwace garin Deir al-Zor na kasar daga hannun 'yan ta'addan Da'esh inda ya ce yana mika sakon godiyarsa ga Jagoran da kuma al'ummar Iran saboda sadaukarwa da goyon bayan da suka ba wa gwamnatinsa a fada da ta'addanci da take yi.

Shugaba Asad ya ce ko shakka babu Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da hannu cikin irin nasarorin da sojojin Siriya suka samu kuma suke ci gaba da samu a kan 'yan ta'addan, yana mai sake jaddada aniyar gwamnati da al'ummar Siriya na ci gaba da fada da ta'addanci da zalunci da babakeren manyan kasashen duniya.

A kwanakin baya ne dai sojojin Siriya da kawayenta na daga dakarun Hizbullah na kasar Labanon da kuma shawarwarin kwararrun sojojin Iran da suke samu bugu da kari kan hare-haren da jiragen yakin Rasha suka kai wa suka sami nasarar kwato garin Deir Zor din da ya kwashe sama da shekaru uku a hannun 'yan ta'addan Da'esh.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky