Shugaban Kasar Rasha Ya Bukaci Sojojin Kasarsa Su Fara Janyewa Daga Kasar Siriya

Shugaban Kasar Rasha Ya Bukaci Sojojin Kasarsa Su Fara Janyewa Daga Kasar Siriya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci sojojin kasar su fara janyewa daga kasar Siriya zuwa gida.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, shugaban ya bayyana haka ne a safiyar yau Litinin a lokacin da ya kai ziyarar ba zata, zuwa sansanin sojojin kasar ta Rasha na Hmeymim  da ke birnin Latakia na kasar Siriya. 

Putin ya kara da cewa sojojin kasarsa sun cimma manufofinsu na wargaza kungiyar 'yan ta'adda da ke kiran kanta "daular musulunci" wato kungiyar Daesh a cikin shekaru biyu da suka gabata,

Shugaban na Rasha ya gana da takwaransa na kasar Siriya a wannan ziyarar ya kuma yi jawabi wa sojojin kasar ta Rasha da ke kasar ta Siriya kafin ya wuce zuwa kasar Masar. 

Rasha ta fara kai hare-hare kan mayakan kungiyar yan ta'adda ta Daesh ne a shekara ta 2015.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky