Shugaban Kasar China Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Afrika

Shugaban Kasar China Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Afrika

Shugaban kasar China ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda a halin yanzu haka ya isa kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya habarta cewa" Shugaban kasar China Xi Jinping a yau Asabar ya isa kasar Senegal a wata ziyarar aiki da zai gudanar a kasashen nahiyar guda hudu da nufin karfafa alakar kasuwanci da na soji tsakanin China da kasashen na Afrika.

A bayan kammala ganawarsa da mahukuntan Senegal; Shugaba Xi Jinping zai zarce zuwa kasar Ruwanda da Afrika ta Kudu, inda a karshe zai karkare ziyarar tasa da Jamhuriyar Mauritius da ke gabar tekun indiya,

Wannan ita ce ziyarar aiki na farko da shugaban kasar China Xi Jinping ya fara tun bayan sake dare karagar shugabancin China a wa'adi na biyu a watan Maris na wannan shekara.   


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky