Shugaban Amurka Ya Bada Umurnin Kara Zafafa Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen

Shugaban Amurka Ya Bada Umurnin Kara Zafafa Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen

Shugaban kasar Amurka ya bada umurni ga Ma'aikatar tsaron Amurka ta "Pentagon" kan kara daukan matakan zafafa kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.

Tashar talabijin ta Sky News ta watsa rahoton cewa: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada umurni ga ma'aikatar tsaron kasar ta "Pentagon" kan daukan matakan zafafa kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen da sunan yaki da ta'addanci.

Tashar ta Sky News ta kara da cewa: A halin yanzu haka shugaba Donald Trump yana duba yiyuwar daukan irin wannan mataki kan kasashen Libiya da Somaliya.

Tun a ranar 25 ga watan Maris shekara ta 2015 ne kasar Saudiyya da kawayenta na kasashen Larabawa gami da tallafin kasar Amurka suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen bayan bullar rikicin siyasar cikin gida a kasar kan shugabanci lamarin da a halin yanzu ya lashe rayukan daruruwan mutane tare da jikkatan wasu dabbun daruruwa bayan ga rusa duk wani abu mai amfani a kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky