Shugaba Ruhani Ya Mayar Da Martani Ga Jawabin Shugaban Amurka Kan Iran

Shugaba Ruhani Ya Mayar Da Martani Ga Jawabin Shugaban Amurka Kan Iran

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar babu wani abu cikin jawabin shugaban Amurka Donald Trump kan Iran face wauta da tuhumce-tuhumce marasa tushe yana mai cewa al'ummar Iran ba za su taba mika wuya ga wani mai takama da karfi da girman kai ba.

Shugaba Hasan Ruhani ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a daren jiya jim kadan bayan jawabin da shugaban Amurka yayi a matsayin sabuwar siyasar Amurka kan kasar Iran inda yayi watsi da kiran da shugaban Amurkan yayi na a sake yin kwaskwarima ga yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya yana mai cewa Iran ba za ta taba amincewa da kari ko rage wani abu a cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma ba.

Shugaba Ruhani ya ci gaba da cewa Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan matukar dai yarjejeniyar ta ci gaba da kiyaye manufofi da hakkokin al'ummar Iran.

Yayin da ya koma kan tuhumar da Trump yayi wa Iran na goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya, shugaba Ruhani yayi ishara da irin rawar da Amurka ta taka wajen kirkiro kungiyoyin ta'addanci irin su Da'esh (ISIS) wanda shi da kansa Trump din ya tabbatar da hakan a yayin yakin neman zabensa bugu da kari kan irin ayyukan wuce gona da iri da Amurkan take ci gaba da yi wa sauran kasashen duniya a yankin Gabas ta tsakiya da Latin Amurka da sauransu.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) da Trump din ya tuhumce su da goyon bayan ayyukan ta'addanci, shugaban na Iran yayi watsi da wannan tuhuma yana mai ishara da irin rawar da dakarun suka taka wajen fada da kungiyoyin ta'addanci a Iraki da Siriya da kuma irin rawar da suke takawa wajen taimakon al'ummomin kasashen Yemen da Labanon. Kamar yadda kuma ya sake jaddada aniyar Iran na ci gaba da karfafa irin karfin kariya da take da shi ciki kuwa har da makamanta masu linzami.

A daren jiya ne dai shugaban Amurkan cikin wani jawabi da yayi ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da yarjejeniyar nukiliya da kuma sanar da sabbin takunkumi a kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky