Shugaba Rauhani Ya Kammala Ziyarar Aiki A Kasar Rasha

Shugaba Rauhani Ya Kammala Ziyarar Aiki A Kasar Rasha

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya kammala ziyarar aiki ta yini biyu da ya gudanar a kasar Rasha.

Da jijjifin safiyar yau ne shugaba Rauhani ya iso filin safka da tashin jiragen sama na Mehrabad da ke birnin Tehran, bayan kammala ziyarar tasa a birnin Moscow, inda ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasar Rasha, da suka hada da shugaba Putin da kuma Firayi ministan kasar Dmitry Medvedev.

A yayin wannan ziyara, an sanya hannu kan yarjeniyoyi 14 a tsakanin Iran da Rasha, da suka danganci bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya, ilimi, tsaro da dai sauransu.

A cikin bayanin karshen ziyarar wanda shugabannin Rasha da Iran da suka fitar, sun jaddada wajabcin ci gaba da karfafa kawancen da ke tsakaninsu da kuma gudanar da ayyuka na hadin gwaiwa domin amfanin al'ummominsu.

Dangane da matsalolin da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya kuwa, shugabannin na Rasha da Iran sun jaddada wajabcin yin amfani da siyasa da hanyoyi na sulhu da fahimtar juna domin warware matsaloli a kasashen da ake fama da rikici, musamman a Syria, kasar da ke fuskantar babbar barazanar ta'addanci, wanda wasu kasashe ke amfani da hakan domin cimma manufofinsu na siyasa a kan gwamnatin kasar ta Syria.

Kamar yadda kuma suka bukaci kawo karshen hare-haren da ake kaddamarwa a kan al'ummar Yemen ba tare da wani bata lokaci ba, wanda hakan ya yi sanadiyyar jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin hali kamar yadda duniya take gani.

Daga karshe shugaba Putin an Rasha ya mika godiya ta musamman ga shugaba Rauhani, da kuma mika sakon gaisuwa ga jagoran juyin Isalama na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, tare da bayyana Iran a matsayin babbar makwabciya ga Rasha, kuma abiyar kawance mai riko da alkawali.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky