Shugaba Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Shugaban Saliyo

Shugaba Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Shugaban Saliyo

Shugaba Hassan Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar saliyo Julius Maada Bio.

Shafin yanar gizo na shugaban kasar Iran ya bayar da bayanin cewa, a cikin sakon da shugaba Rauhani ya aike wa sabon shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana cewa; yana taya sabon shugaban kasar murna kan nasarar da ya samu, kuma yana yi masa fatan alhairi da samun nasara wajen gudanar da dukkanin ayyukansa, domin ci gaban kasar Saliyo da al'ummarta baki daya.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya bayyana kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen Iran da saliyo da cewa, alaka ce daddiya, kuma za ta ci gaba da kara bunkasa a dukkanin bangarori, na siyasa, tattalin arziki, kasuwanci da al'adu da sauransu.

Kasar Saliyo dai na daga cikin kasashen yammacin Afirka da suke da kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasar Iran, kamar yadda kuma suke da huldodi na kasuwanci da tattalin arziki.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky