Shugaba Rauhani Na Iran Ya Isa Birnin Moscow Na Rasha

Shugaba Rauhani Na Iran Ya Isa Birnin Moscow Na Rasha

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yammacin yau, a ziyarar kwanaki biyu da zai gudanar a kasar bisa gayyatar da shugaba Putin ya aike masa.

Shugaba Rauhani ya isa babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Moscow a yammacin yau, inda a daren yau zai gana da Firayi ministan kasar ta Rasha Dmitry Medvedev.

A safiyar gobe Talata kuma zai gabatar da jawabi a babbar jami'ar Moscow ga malaman jami'ar da kuma masana da za su halarci wurin, inda jami'ar za ta bayar da digirin digirgir na girmamawa ga shugaba Rauhani.

Haka na  kua a gobe ne da rana zai isa fadar shugaba Vladmir Putin, inda za su gudanar da tattaunawa a kan batutuwa da dama da suka shafi alaka a tsakanin Iran da Rasha, musamman a bangarorin harkokin tattalin arziki da cinikayya da sauran ayyuka a fagen ilimi da kuma tsaro, haka nan kuma za su duba sauran batutuwa da suka shafi ayyuka na hadin gwiwa da suke yi tare musamman a fagen yaki da ta'addanci a Syria.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky