Shugaba Buhari Ya Bukaci ICC Ta Yi Wani Abu Dangane Da Shari'ar Masu Sama Da Fadi Da Kudaden Jama'a

Shugaba Buhari Ya Bukaci ICC Ta Yi Wani Abu Dangane Da Shari'ar Masu Sama Da Fadi Da Kudaden Jama'a

Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya bukaci hukumar ICC ko kotun duniya ta yi wani abu don taimakawa yaki da cikin hanci da rashwa a kasashen duniya don gainin bayan wannan annubar.

Jaridar daily trust ta Nigeria ta nakalto shugaban yana fadar haka a bukin cika shekaru 20 da kafa hukumar ta ICC a birnin a birnin Haque, a kasar Netherland a jiya Talata. Shugaban ya kara da cewa daukar matakan da suka dace masu kwari zai taimakawa sauran kokarin da wasu bangarori suke yi na yakar wannan annubar.

Muhammadu buhari ya kara da cewa a dai dai kungiyar tarayyar Afrika take kokarin a wannan bangaren tana bukatar ganin a sanya birki da kudaden sara da suke  shiga wasu kasashe ba ta hanyoyin da suka dace ba kokuma na sata. Ya ce kokarin hukumar ta ICC zai taimakawa kokarin tabbatar da adalci a kasashen duniya.

Ya bukaci hukumar ta yi aiki tare da sauran kasashen membobi a duniya don yakar wannan annobar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky