SHUGABA BUHARI YANA NUNAWA MUSULMUN NAJERIYA BABBANCI

SHUGABA BUHARI YANA NUNAWA MUSULMUN NAJERIYA BABBANCI

SHUGABA BUHARI YANA NUNAWA MUSULMUN NAJERIYA BABBANCI~~~ CEWAR ATTAHIRU MUHAMMAD MARNONA SARKIN YAKIN BUHARI:

Nayi matukar kaduwa da  rasa abin da zan Kare Shugaba buhari, bayan na karanta labarin cewa Shugaban  ya amince da fitar da kudi har Naira Bilyon 10bn domin gyara muhallan da aka lalata na  'yan Kabilar Birom da rikicin addini ya shafa a Jihar Plateau.


Sarkin yakin buharin Yaci gaba da cewa   An yiwa Fulani Musulmi barna wacce ta ninka ta Birom a Mambilla ta Jihar Taraba, an yiwa Hausawa da Fulani barnar da tafi Wannan a Jihar Zamfara, anyi a Birnin Gwari, anyi a Numan, duk wadancan kashe-kashen  Shugaban Kasa bai ware ko dubu biyar ba da niyar a taimaka musu,  shin su ba yan Nigeria bane? Ko ba su da hakken a taimake su?


 

To wallahi Buhari kaji  tsoron Allah ka  sani cewa Allah zai tambaye ka  akan wannan Abin da yake faruwa,  domin karara kana  nunawa musulmi babbancin Addini, kuma ka nuna rayukan Musulmi ba a  bakin komai suke  ba.


Don haka a matsayin mu na masoyan   Shugaban kasa kuma masu nunawa mutane cewa shi mai gaskiya ne dole mu gayamasa gaskiya, domin ya sani ran Kiristoci bai fi na Musulmi ba.


Daga karshe Sarkin yakin ya cigaba da cewa   tsarin dokokin kasarnan  baya nuna ban banci, don haka ran kowa dayane a Najeriya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky