Sharhi: Kisan Musulmi Fiye Da 2000 A Cikin Mako Guda A Kasar Myanmar

Sharhi: Kisan Musulmi Fiye Da 2000 A Cikin Mako Guda A Kasar Myanmar

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama ne suke bin diddigin abin da yake faruwa na kisan kiyashin da ake yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar, musamman ma acikin kwanakin nan da lamarin yake kara tsananta.

Kungiyar kare kare hakkin bil adama ta Fortify Rights, daya ce daga cikin manyan kungiyoyin kare hakkin bil adama a gabashin nahiyar Asia, dake da babban ofishinta  birnin bankuk na kasar Thailand. A cikin rahoton da wanann kungiyar ta bayar a jiya Lahadi, ta bayyana cewa ta ji ta bakin daruruwan mutane daga cikin dubban musulmi 'yan kabilar Rohingya da suka tsere daga muhallansu suka shiga cikin kasar Bangaladesh a cikin wannan mako.

Daga cikin mutanen akwai wdanda sun rasa 'ya'yansu, wasu kuma sun rasa iyayensu, wasu sun rasa danginsu, sakamakon hare-haren da sojojin gwanatin Myanmar tare da mabiya addinin Buda masu tsatsauran ra'ayi suka kaddamar a kansu a cikin wannan mako.

Wadanda suka sheda lamarin sun ce jami'an sojin gwamnatin Myanmar sun kai farmaki a ranar Juma'a 25 ga watan Agustan da ya kare a kauyen Chut Pyn dake cikin yankin Rathedaung, inda suka kashe daruruwan mata da kananan yara, ta hanyar jefa su a cikin wuta suna kona su, kamar yadda kuma sukan yi amfani da manyan adduna wajen sare kawunan duk wani musulmi da suka gani a yankin, sun kona dukkanin gidajen musulmi da ke yankin baki daya, tare da dukkanin kaddarorinsu.

A nasa bangaren shugaban kungiyar musulmi 'yan kabilar Rohingya  mazauna nahiyar turai Anita Shug ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Anatoli a jiya cewa, bisa rahotannin da suk tattara dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a kasar Myanmar, an rusa tare da kone dubban gidajen musulmi tare da kashe fiye da dubu biyu a cikin kimanin mako guda da ya gabata a cikin gundumar rakhin kawai, yayin wasu fiye da dubu 100 kuma suka tsere suka bar yankunansu domin tsira da rayuwarsu, ba tare da sanin inda za su nufa ba, wanda hakan yasa wasu daga cikin su suke mutuwa  a hanya, sakamakon raunuka da suka samu, ko kuma yunwa da rashin abicnin da za su ci, yayin da wasu suke mutuwa a cikin koramu a lokacin da suke tsallakawa domin tsira daga hare-haren sojojin gwamnatin Myanmar, musamman mata da kananan yara.

Wannan lamari ya daga hankula al'ummomin duniya, wanda hakan yasa wasu daga cikin kasashen musulmi irin su Indonesia, Iran, Turkiya gami Kazakhstan, suka zauna jakadan kasar Myanmar majalisar dinkiin duniya a birnin new York, inda suka jan kunnen gwamnatin Myanmar kan wannan mummunan aiki na kisan kiyashi da sojojinta ke yi a kan musulmi, tare da kiran majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar kasashen msuulmi kan su sanya hannu a cikin lamarin domin ganin an tilasta Myanmar kan dakatar da kisan musulmi a kasar.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin ta Myanmar ta musunta cewa adadin mutanen da aka kashe ya haura daruruwa, kamar yadda kuma ta ce gidaje 2600 ne kawai na musulmi aka rusa ko  kuma aka kone, tare da bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan lamarin kamar dai yadda ta saba fadi,a  matsayin wata hanya ta yawo da hankulan al'ummomin duniya a kan wannan batu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky