Sayyid Nasrallah Ya Ja Kunnen 'Yan Da'esh Da Su Bar Labanon Tun Lokaci Bai Kure Musu Ba

Sayyid Nasrallah Ya Ja Kunnen 'Yan Da'esh Da Su Bar Labanon Tun Lokaci Bai Kure Musu Ba

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya jinjinawa dakarun kungiyar saboda nasarar da suka samu na fatattakan 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra daga kasar yana mai jan kunnen 'yan kungiyar Da'esh da su yi kiyamul laili wa kansu su bar kasar tun lokaci bai kure musu ba.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a daren jiya don sanar da samun nasarar karshe a kan 'yan ta'addan Jabhatun Nusra da suke rike da yankin Arsal na kasar Labanon din na kimanin shekaru uku, yana mai jan kunnen 'yan kungiyar Da'esh da suke rike da wani bangare na kasar da cewa su gaggauta barin kasar ko kuma a fitar da su da karfin tuwo kamar yadda dakarun Hizbullah din suka fatattakin 'yan Jabhatun Nusra da karfin tuwo.

A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Nasrallah ya jinjinawa irin goyon bayan da 'yan kungiyar Hizbullah suka samu daga wajen shugaban kasar Labanon, shugaban majalisar kasar da kuma firayi ministan kasar Labanon din, bugu da kari kan irin goyon baya da taimakon da kasar Iran ta ba wa kungiyar wajen fada da 'yan kungiyar ta'addancin.

A ranar Juma'ar makon da ya wuce ne dakarun kungiyar Hizbullah din suka kaddamar da wasu gagaruman hare-hare kan 'yan kungiyar Jabhatun Nusra da suka mamaye wani yanki na kasar Labanon din inda cikin 'yan kwanaki suka fatattake su. A halin yanzu kuma ana ta kan shirye-shiryen fatattakan 'yan kungiyar Da'esh da su ma suka mamaye wasu yankuna na Labanon din.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky