Saudiyyah Ta Ce Maniyyata Daga Iran Za Su Safke Faralin Hajjin Bana

Saudiyyah Ta Ce Maniyyata Daga Iran Za Su Safke Faralin Hajjin Bana

Gwamnatin kasar Saudiyyah ta ce maniyyata daga kasar Iran za su halarci aikin da za a gudanar a wannan shekara.

kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyyah SPA ya bayar da rahoto a yammcin yau cewa, ma'aikatar kula da ayyukan hajji da umrah ta Saudiyyah ta sanar a yau cewa, maniyyata daga kasar Iran za su halarci ayyukan hajjin bana.

Ma'aikatar kula da ayyukan hajjin ta Saudiyya ta ce wannan ya biyo bayan tattaunawar da aka gudanar tsakanin bangarorin biyu ne kan cimma matsaya dangane da wannan batu.

A cewar bayanin, dukkanin bangarorin sun amince da cewa za su yi aiki da abin da suka cimma matsaya  akansa kan batun aikin hajjin.

A shekarar da ta gabata alhazan kasar Iran ba su samu damar safke farali ba, sakamakon kin ba su izinin shiga cikin kasar ta Saudiyya, bayan da aka kasa cimma matsaya tsakanin Iran da kuma kasar ta Saudiyya, inda Iran ta bukaci gwamnatin Saudiyya ta bata tabbaci kan cewa za a kare rayukan dukkanin alhazanta, domin kauce wa kara faruwar mutuwar alhazai a Mina, amma gwamnatin Saudiyya ta ce ba za ta ba Iran tabbacin kare rayukan alhazanta ba.

A hajjin shekara ta 2015 fiye da alhazai dubu 7 suka rasa rayukansu, da suka hada da daruruwan alhazan kasar Iran, da kuma daruruwan alhazan Najeriya da wasu kasashen Afirka da na Asia, sakamakon rashin tsarin da aka samu daga masu shirya wuraren da ake gudanar da jifar shedan a Mina.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky