Saudiyya: Za a yankewa wata mai fafutukar rajin kare hakin bil'adama hukuncin kisa

Saudiyya: Za a yankewa wata mai fafutukar rajin kare hakin bil'adama hukuncin kisa

Rahotanni sun ce masu shigar da kara a Saudiyya sun bukaci a yanke hukuncin kisa ka masu fafutika biyar, cikin su har da mai fafutikar kare hakkin mata Israa al-Ghomgham.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce a kwanakin baya ne wata kotun da ke yanke hukunci kan ayyukan ta'addanci ta tuhume su da laifin shiga zanga-zanga a yankin Qatif.

Galibin mazauna yankin 'yan Shia ne marasa rinjaye kuma ya yi kaurin suna wajen yawaita gudanar da zanga-zanga.

An yi amannar cewa Ms Ghomgham ita ce 'yar kasar Saudiyya ta farko da take fuskanat hukuncin kisa saboda ayyukanta na kare hakkin mata.

Human Rights Watch ta yi gargadin cewa hukuncin da aka yanke mata "zai haifar da mummunan sakamako ga sauran masu rajin kare hakkin mata da ke daure a gian yari." kasar.

Mahukuntan kasar ta Saudiyya sun daure akalla masu kare hakkin dan adam da na mata 13 tun daga tsakiyar watan Mayu, inda ake zargin su da yin ayyukan da ke barazana ga tsaron kasa. An saki wasu daga cikin su ko da yake har yanzu wasu na tsare ba tare da an tuhume su ba.Human Rights Watch ta ce Ms Ghomgham mai fafutika ce da ta yi fice kan shigea gaba a zanga-zanga da ke faruwa a Qatif tun 2011.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky