Saudiyya Ta Haramta wa Maniyyata Daga Qatar Sauke Farali A Wannan Shekara

Saudiyya Ta Haramta wa Maniyyata Daga Qatar Sauke Farali A Wannan Shekara

Kwamitin kare hakkokin 'yan kasa a kasar Qatar ya sanar da cewa,a shekarar bana Saudiyya ta haramta wa maniyyata daga kasar ta Qatar zuwa aikin hajji domin sauke farali, saboda dalilai na siyasa.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Abdullah Ka'abi, daya daga cikin mambobin kwamitin kare hakkokin 'yan kasa a Qatar ya tabbatar mata da cewa, gwamnatin kasar ta Saudiyya ta dauki wasu kwararan matakai a kan maniyyata na kasar Qatar, da hakan ya haramta musu zuwa aikin hajjin bana.

Ya ce daga cikin matakan kuwa, har da toshe safin yanar gizo da Saudiyya ta bude domin bayar da visa ga maniyyata daga kasar Qatar, wanda babu wata hanya da za su iya karbar izinin shiga kasar ta wannan hanyar.

Saudiyya ta dauki matakin hana alhazan kasar Qatar zuwa aikin bana ne sakamakon takun saka na siyasa da ke tsakanin gidajen sarautar kasashen biyu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky