Saudiyya Ita Ce Tushen Tsaurin Ra'ayi Da Ta'addanci

Saudiyya Ita Ce Tushen Tsaurin Ra'ayi Da Ta'addanci

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, kasar Saudiyya ita ce tushe kana kuma mahaifar tsaurin ra'ayi da ayyukan ta'addanci, sannan kuma babbar alama ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidajen kasashen yankin Gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin Farsnews ya bayyana cewar kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a yayin da yake mayar da martani ga kalaman ministan harkokin wajen Saudiyya Adel Al-Jubair inda ya ce siyasar rashin sanin ya kamata da Saudiyya take gudanarwa shi ne tushen ayyukan ta'addanci da rashin kwanciyar hankali da yankin Gabas ta tsakiya ke fama da shi.

Mr. Qassemi ya kara da cewa ministan harkokin wajen Saudiyya yana kokarin rufe gaskiya ne kawai kamar yadda suka saba wajen tuhumar wasu da goyon bayan ayyukan ta'addanci alhali su ne masu goyon bayan 'yan ta'addan.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce ministan harkokin wajen Saudiyyan cikin wata hira da yayi da tashar CNBC ya bayyana cewar Saudiyya tana fatan ganin an kara matsin lamba da sanya takunkumi wa Iran saboda goyon bayan ayyukan ta'addanci da kuma karya kudurin kwamitin tsaro kan makamanta masu linzami.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky