Sakon Jagora Na Sabuwar Shekara Hijirar Shamsiya 1396

Sakon Jagora Na Sabuwar Shekara Hijirar Shamsiya  1396

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar Iran a kan shiga Sabuwar Shekara Iraniyawa ta 1396 Hijira shamsiya da aka shiga yau Litini.

A Sakonsa na sabuwar shekara, Ayatollah Khamenei, ya soma da gabatar da murnarsa dangane da zagayowar ranar haihuwar 'yar Manzon tsira, Fatima Zahra (AS), tare da kuma fatan wannan sabuwar shekara ta zamanto mai cike da tarin albarka da tsaro ga dukkan al'ummar Iraniyawa kama daga iyalan shahiddan kasar da wadanda suka samu raunuka a wajen yaki, dama duk sauran al'ummar musulmi. 

Ayatollah Khamenei ya kira sabuwar shekara ta kalandar Iraniyawa da taken '' shekarar tattalin arziki da juriya da kuma samar da ayyukan yi''

Jagoran ya kara da cewa ''duk da cewa matsalar tsaro na barazana ga kasar mu da kasashe makwafta da kuma yankin, ba mu taba yin wasa ba da al'amurran tsaro, kuma al'ummar kasarmu ta fahimci mine ne tabbatar da tsaro mai dorewa''

Sai dai a cikin jawabin nasa Ayatollah Ali Khamenei, ya soki yadda gwamnatin kasar ke tafiyar da al'amuran tattalin arziki.

A sakon nasa ya ce yana da masaniya, kana kuma yana jin takaici dangane da halin da talakawa ke ciki, wanda ya danganta da kasawar gwamnatin kasar na biyan bukatun al'ummarta.

Ayatollah Ali Khamenei, ya kara da cewa akwai sakamako mai kyawo ta fuskar tattalin arzikin gwamnati, amma akwai tazara mai yawa tsakanin abin da aka yi da abin da al'umma suka yi fatan gani daga gwamnati.

Jagoran ya zayyano matsalolin da suka hada rashin aikin yi, tsadar rayuwa, rashin daidaito da kuma matsalolin zamantakewa da ya ce mu dukkanmu muke fuskanta wadanda kuma a cewarsa dole mu dogara da Allah da al'ummarmu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni