Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)

Matanin sakon jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga mahajjata na wannan shekara.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu, Cikamakin Annabawa tare da Alayensa tsarkaka da Sahabbansa zababbu.

Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da a wannan shekarar ma Ya ba wa wani adadi mai yawa na muminai daga dukkanin fadin duniya damar gudanar da aikin hajji don su sami damar amfanuwa da kuma sha daga wannan mabubbugar ruwa mai albarka sannan kuma su sami damar makwabtakar Dakin Allah Mai alfarma da gudanar da ibadu, addu'oi, zikiri da kuma neman kusaci da Allah Madaukakin Sarki a wadannan ranaku wadanda dararen da sa'oinsu, za su iya sauya zukata da tsarkake su.

Aikin Hajji, wata ibada ce da take cike da sirruka, haka nan Dakin Allah mai alfarma, wani waje ne da ke cike da albarkoki na Ubangiji kana kuma mazhari na ayoyi da alamu na Allah Madaukakin Sarki. Aikin Hajji yana iya kai muminin bawa, ma'abocin kankan da kai da tunani zuwa ga matsayi na kusaci da Allah da kuma matsayi na daukaka da haske; kamar yadda kuma zai iya mayar da shi ya zamanto wani mutum ma'abocin basira da jaruntaka kana kuma mai aiki tukuru ba kama hannun yaro. Dukkanin wadannan bangarori biyun, wato na ruhi da siyasa, ko kuma na daidaiku da na al'ummance (na zamantakewa) ana iya ganinsu a fili cikin wannan farali maras tamka, wanda kuma a halin yanzu al'ummar musulmi suna tsananin bukatar dukkanin wadannan bangarori biyun.

A bangare guda kuma masu bautar abin duniya sun dukufa ta hanyar amfani da hanyoyi da kayan aiki na zamani wajen haifar da fasadi da badala, sannan a bangaren guda kuma 'yan mulkin mallaka suna ta aikin haifar da fitina da rarrabuwan kai tsakanin musulmi da mayar da kasashen musulmi suka zamanto tamkar wata tunga ta sabani da rashin tsaro. Aikin Hajji yana iya zama wani magani ga dukkanin wadannan bala'oi guda biyu da suka fada wa al'ummar musulmi; wato zai iya tsarkake zukata daga tsatsa da kuma haskaka su da hasken tsoron Allah da masaniyarSa; kamar yadda kuma zai iya bude idanuwa da nuna musu hakikanin yanayi mai bakanta rai da duniyar musulmi take ciki sannan kuma ya karfafa azamar da ake da ita ta fada da hakan da kuma shiryar da hannuwa da kwakwale wajen zama cikin shirin aiki.

A yau duniyar musulmi tana fuskantar matsalar rashin tsaro; rashin tsaro na kyawawan halaye da abubuwa masu kyautata ruhi da kuma rashin tsaro na siyasa. Babban ummul aba'isin hakan kuwa ita ce gafalarmu da kuma makirce-makircen makiya. Dangane da batun makirce-makircen makiya lalle mun gaza wajen sauke nauyi na addini da hankali da ke wuyanmu; mun mance da (fadin Allah) " Su (musulmi) masu tsanani ne ga kafirai", haka nan da "Masu rahama da tausayi a tsakaninsu". Sakamakon hakan kuwa shi ne cewa har ya zuwa yanzu sahyoniyawa nakiyan al'umma suna ta haifar da fitina a tsakiyar duniyar musulmi alhali mu kuma mun gafala daga nauyin 'yantar da kasar Palastinu da ke wuyanmu, mun shagaltu da yakin basasa a kasashen Siriya da Iraki da Yemen da Libiya da Bahrain da kuma fada da ta'addanci a Afghanistan da Pakistan da sauransu.

Ko shakka babu shugabannin kasashen musulmi da 'yan siyasa da malamai da masanan duniyar musulmi suna ga gagarumin nauyi a wuyansu, da suka hada da: nauyin samar da hadin kai da nesantar rikice-rikice na kabilanci da mazhaba; nauyin wayar da kan al'umma dangane da hanyoyin da ma'abota girman kan duniya da yahudawan sahyoniya suke bi wajen haifar da kiyayya da gaba a tsakaninsu; nauyin tattaro karfi waje guda da nufin fada da makiya a fagage daban-daban na yaki, yaki na makamai da na kwakwalwa; nauyin dakatar da bala'in da ya fada wa duniyar musulmi cikin gaggawa, wanda misalin hakan shi ne abubuwa masu sosa rai da ke faruwa a kasar Yemen da ke ci gaba da bakanta ran al'ummomi da kuma fuskantar tofin Allah tsine; nauyin ba da kariya ga musulmi 'yan tsirarru da suke fuskantar zalunci, kamar musulman kasar Myammar da ake zalunta da sauransu; sannan kuma mafi muhimmancin cikinsu shi ne ba da kariya ga Palastinu da nuna goyon baya dari bisa dari ga al'ummomin da kusan shekaru saba'in kenan suke gwagwarmaya wajen kwato kasarsu da aka mamaye.

Wadannan nauyi ne masu muhimmanci da suke wuyayen dukkaninmu. Wajibi ne al'ummomi su bukaci hakan daga gwamnatocinsu, sannan su kuma masana su tsaya kyam cikin kyakyawar niyya wajen ganin an cimma hakan. Wadannan ayyukan, misali ne na hakika na taimakon addinin Allah, wanda ko shakka babu, kamar yadda Allah Ya yi alkawari, zai kawo nasa daukin.

Wadannan wasu bangarori ne na darussan aikin Hajji da fatan za mu fahimce su da kuma aiki da su.

Ina roka muku karbabben hajji daga wajen Allah Madaukakin Sarki, kamar yadda kuma na ke kara jinjinawa shahidan Mina da Masjid al-Haram ina mai roka musu karin girman matsayi a wajen Allah Mai jin kai da karimci.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.

 

Sayyid Ali Khamenei

 

7, Shahrivar, 1396 H S

 

7, Zul Hajj, 1438 H K

 

(29, Augusta, 2017)


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni