S. Nasrallah: Saudiyya Ta Girmama Trump Ne Don Samun Goyon Bayan Yakar Iran

S. Nasrallah: Saudiyya Ta Girmama Trump Ne Don Samun Goyon Bayan Yakar Iran

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana taron da Saudiyya ta shirya don maraba da shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin wani kokari na girmama Trump din da kada kugen yaki a kan kasar Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmaya yana mai cewa hakan babu abin da zai kara musu face tsayin daka kan tafarkin da suke kai.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron bikin zagayowar shekarar da dakarun Hizbullah din suka 'yantar da kudancin kasar Labanon din daga hannun yahudawan sahyoniya inda yayin da yake magana kan taron Riyadh da ya gudana tsakanin shugaban Amurka Trump da Sarkin Saudiyya Salman, Sayyid Nasrallah ya ce Saudiyya ta shirya wannan taron ne don girmama Trump din don ta sami wata kariya daga wajen Amurkan don kuwa a halin yanzu kowa ya san ita ce babbar mai kare 'yan ta'adda da kuma yadda ta'addanci a duniya.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa wata manufar kuma ta gaba na wannan taron shi ne kaga kugen yaki a kan Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmayar irin su Hizbullah da Hamas da sauransu da Saudiyyan ta sa a gaba, yana mai cewa ko shakka babu wannan aiki na Saudiyya zai zama aikini baban giwa don kuwa Saudiyyan tana ci gaba da shan kashi a dukkanin abin da ta sa a gaba kama daga kasar Iraki, Siriya da Yemen da sauransu.

Sayyid Nasrallah ya ci Saudiyyan ta ba wa Trump din dukkanin abin da yake bukata saboda shirinta na yakar Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmayar alhali shi kuwa Trump abin da ya dame shi ne shi ne dukiya da kuma kare haramtacciyar kasar Isra'ila.

A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Nasrallah yayi kakkausar suka ga ci gaba da diran mikiya da masarautar Al Khalifa ta ke yi a kan al'ummar Bahrain musamman barazanar da take yi wa rayuwar babban malamin kasar Sheikh Isa Qasim.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky