Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Yi Sanadiyar Rayuka a Adamawa

Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Yi Sanadiyar Rayuka a Adamawa

Mutane sama da 10 aka kashe a wani tashin hankali da ya faru tsakanin makiyaya da al’ummar Bachama da suka kasance manoma, a yankin Gwamma na karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa.

Kamar yadda rahotanni ke nunawa, fiye da rayuka 13 ne suka salwanta a wannan tashin hankali da ake dangantawa da ramuwar gayya wanda ya faru a yankin Gwamma da ke karamar hukumar Demsa, na jihar Adamawa.

Cikin wadanda aka kashe har da wani tsohon kwamishina, kuma kakakin jam’iyar PDP a jihar Mr.Sam Zadok, wanda a kwanakin baya aka ji muryarsa a cikin shirin Muryar Amurka na Tsaka Mai Wuya, game da rikicin al’umman Bachama da Fulani Makiyaya.

Shugaban matasan Bachama, Euphraimu Paul Turaki, ya tababtar da aukuwar wannan lamari.

Abdullahi Adamu Prembe, wanda sakataren jam’iyar PDP ne a jihar, ya bayyana wannan tashin hankali a matsayin abin takaici, yana mai kira ga hukumomi da su tashi tsaye, musamman a wannan lokaci.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa, SP Othman Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ko da yake, ya ce rundunar ba ta da cikakken alkaluman wadanda suka raswa rayukansu ya zuw yanzu


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky