Rauhani: Trump Na Son Kawo Rudani A Iran

Rauhani: Trump Na Son Kawo Rudani A Iran

Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa manufar firicin shugaban kasar Amurka na baya-bayan nan musamam ma tayin tattauna da Iran sanya rudani a tsakanin al'ummar Iran.

A daren jiya Litinin ne shugaban kasar Iran Dakta hasan Rouhani ya bayyana a gaban talabijin din kasar inda ya fadawa al'ummar kasar cewa a ganinsa manufar shugaba Trump na Amurka na firicin baya-bayan nan kan kasar Iran musaman ma tayin tattaunawa da kasar, sanya rudani da kokonta a tsakanin al'ummar kasar, sannan a bangare guda yin amfani da dama wajen neman kuri'u a zaben 'yan Majalisa na kasar za a gudanar a watani masu zuwa.

Yayin da yake ishara kan matsalar da Amurka ta shiga bayan ficewarta daga yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiya na Iran da aka cimma tsakanin manyan kasashen Duniya, Shugaba Rouhani ya bayyana cewa a halin yanzu Shugaba Trump na kokarin dawo da mutuncin Amurka ne ta hanyar tayin tattunawa da kasar Iran.

Shugaban Rouhani ya bayyana cewa wanda yake da'awar cewa a shirye yake ya tattauna da Al'ummar Iran ya san cewa ko wata irin tattaunawa ta ginu ne a kan gaskiya, amma mutuman da ya fice daga yarjejjeniyar kasa da kasa ba tare da tattaunawa ba, sake tattauna da shi ba ta da amfani.

Har ila yau shugaba Rouhani ya bayyana cewa cikin shekaru 40 na juyin musulinci, kasar Amurka na amfani da duk wata dama da ta samu na cutar da kasar Iran.

A bangare guda Shugaba Rouhani ya bayyana shirin da gwamnatinsa ta dauka na magance matsalolin tattalin arziki bayan sabin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky