Rauhani: Bakar Siyasar Amurka A Kan Iran Ba Za Ta Yi Nasara Ba

Rauhani: Bakar Siyasar Amurka A Kan Iran Ba Za Ta Yi Nasara Ba

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya bayyana cewa; bakar siyasar Amurka a kan kasar Iran ba za ta taba yin nasara ba.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a jiya a gaban babban taron majalisar dinkin duniya karo na 73, wanda yake gudana a babban zauren majalisar da ke birnin New York na kasar Amurka.

Rauhani ya ci gaba da cewa; siyasar Amurka dangane da kasar Iran tana cike da kurakurai, kamar yadda kuma irin wannan salon siyasar ya jefa dokokin kasa da kasa cikin hadari, domin kuwa Amurka tana karya dokokin duniya yadda ta ga dama, inda ya bayar da misali da yadda Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimmawa tare da Iran, wadda majalisar dinkin duniya ta fitar da kudi mai lamba 2231 wanda ya mayar da ita yarjejeniyar ta duniya da aka amince da ita.

Ya ce bayan Amurka ta fice daga wannan yarjejeniya ta duniya kan shirin nukliyar kasar Iran, ta kuma koma ga salon siyasar kakaba takunkumi a kan Iran, duk kuwa da cewa babu wani dalili da Amurka ta dogara da shi a kan hakan, domin kuwa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar da rahotanni 12, wadanda suke tabbatar da cewa Iran ba ta yi wani abu wanda ya sabawa ka'ida ko doka a shirin nata ba bisa ga yarjejeniyar da aka cimmawa da ita.

Ya ci gaba da cewa ta'addanci da siyasar kakaba takunkumi duk abu daya ne, domin manufar su ita ce cutar da al'ummomi bisa zalunci, a kan haka Rauhani ya ce yana kiran Amurka da ta gyara salon siyasarta ta neman cutar da al'ummomin duniya da kuma bautar da su saboda tana da karfi, domin wannan salon ba zai taba yin nasara ba.

Rauhani ya ce babu batun tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a halin yanzu, kuma dole ne Amurka ta mutunta dokoki, ka'idoji da yarjeniyoyi na kasa da kasa, kuma ta koma cikin yarjejeniyar shirin  nukiliya kasar Iran wadda ta rattaba  a hannu a kanta, kafin duk wani batun neman ganawa da mahukuntan kasar Iran.

Dangane da batun yakin Syria kuwa, Rauhani ya ce tun daga lokacin da aka haifar da rikici a Syria, Iran ta nuna rashin amincewarta da shigar kasashen duniya a rikin kasar ta Syria, kuma Iran ta shiga Syria ne bayan da gwamnatin kasar ta bukaci hakan a hukumance, wanda kuma hakan bai saba wa wata doka ta duniya ba.

A lokacin da yake magana kan yakin Yemen kuwa, Rauhani ya ce kisan kiyashin da masu yunkurin mamaye kasar Yemen suke yi ya wuce hankali, domin kuwa sun kashe dubban mata da kananan yara da rusa duk wani abu mai amfani a kasar,

, ya ce hanyar warware rikicin kasar Yemen ita ce a bar al'ummar kasar su zauna a tsakaninsu su fahimci juna su warware matsalolinsu ba tare da tsoma musu baki ba.

A kan batun Palastinu kuma Rauhani ya ce haramtacciyar kasar Isra'ila tana yin abin da take yi kan al'ummar Palastinu tare da cikakken goyon bayan Amurka.

Danganhe da batun harin birnin Ahwaz kuma ya bayyana cewa, wasu daga cikin kasashen larabawan yankin ne suka dauki nauyin harin ta'addancin, da nufin dagula lamarin tsaro a cikin Iran, a daidai lokacin da Iran take fatan ganin ta kyautata alaka da dukkanin kasashen yankin domin a samu zaman lafiya da fahimtar da juna.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky