Rasha Zata Mikawa Syria Makamai Masu Garkuwa

Rasha Zata Mikawa Syria Makamai Masu Garkuwa

Kasar Rasha ta sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta mikawa gwamnatin Siriya makaman garkuwa na S-300.

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar ta ce Shugaban kasar ne Vladimir Putin, ya bayyana wa takwaransa na Siriya Bashar Al'Asad hakan a wata zantawa ta wayar tarho.

Sanarwar ta ce nan da 'yan nakwanni za'a mikawa Siriya da makaman.

Wannan dai ya biyo bayan kwana guda bayan cikakken rahoto da Rasha ta fitar dangane da yadda aka harbo jirgin yakinta a lardin Lazikiyya na kasar Siriya wanda ta dora alhakin faruwar hakan a wuyan Isra'ila.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky