Rasha Ta Yi Gargadi Dangane Da Wani Yunkurin Yin Amfani Da Makami Mai Guba A Syria

Rasha Ta Yi Gargadi Dangane Da Wani Yunkurin Yin Amfani Da Makami Mai Guba A Syria

Ma'aikatar tsaron Rasha ta bankado wasu bayanan sirri da suke tabbatar da cewa, Amurka da Birtaniya gami da Faransa suna shirin sake yin amfani da makamai masu guba a Syria, domin su tuhimi gwamnatin kasar ta Syria da yin hakan.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da suke Syria sun shirya tsaf domin yin amfani da makamai masu guba a cikin Syria tare da taimakon Amurka, Birtaniya da kuma Faransa, kuma za a tuhumi gwamnatin Syria ne da yin hakan, domin samun hujjar kai mata hari.

Bayanin ma'aikatar tsaron kasar Rasha ya ce, yanzu haka wani babban jirgin ruwan yaki na Amurka USS Sullivan ya shigo cikin yankin gabas ta tsakiya, kuma ya sauke wani jirgin mai jefa bama-bamai samfurin B-1B a kasar Qatar.

Rahoton ya ce wadannan kasashe suna son su sake maimaita wasan kwaikwayon da suka shirya ne a 'yan watanni baya tare da kungiyoyin 'yan ta'adda, a lokacin da sojojin Syria suka fitar da su daga yankin Ghota, inda yanzu kuma sojojin Syria suke shirin fitar da 'yan ta'adda daga babbar tungarsu da ke Idlib, kuma a nan ne ake son yin amfani da wadannan makamai a kan jama'a fararen hula, domin a karya gwiwar sojojin kasar Syria.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky