Rasha Ta Gargadi Amurka Kan Yin Kafar Angulu Ga Yarjejeniyar Shirin Nukiliya Na Iran

Rasha Ta Gargadi Amurka Kan Yin Kafar Angulu Ga Yarjejeniyar Shirin Nukiliya Na Iran

Gwamnatin kasar Rasha ta gargadi Amurka kan aiwatar da duk wani abu da ka iya kawo cikas ga yarjejeniyar da aka cimmawa a kan shirin Iran na nukiliya.

A cikin wani bayani da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar a jiya, ta bayyana cewa; ya rataya kan Amurka ta yi aiki da yarjejeniyar da aka cimmawa tare da ita da sauran manyan kasashe a kan shirin Iran na nukiliya, kamar yadda dukkanin sauran bangarorin suke yin aiki da wannan yarjejeniya

Bayanin na ma'aikatar harkokin wajen Rasha ya ce, cimma yarjejeniya a kan shirin na nukiliya, na daya daga cikin  ayyuka na diflomasiyya mafi muhimmanci da manyan kasashen duniya suka aiwatar a wannan lokaci, wanda wajibi ne a kan dukkanin bangarori su yi aiki da wannan yarjejeniya kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

Tun bayan da Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin Amurka, yake barazanar yin watsi da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, lamarin da Rasha, da China gami da kungiyar tarayyar turai suke ce ba za su taba amincewa da shi ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds hanyar Shahidai
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky