Rasha Ta Gargadi Amruka Akan Sabon Takumkumi Da Tasa Mata

Rasha Ta Gargadi Amruka Akan Sabon Takumkumi Da Tasa Mata

Fira ministan Rasha ya gargadi kasar Amurka kan sake kakaba takunkumi kan kasarsa da cewa: Kakaba takunkumin yana matsayin shelanta yakin kasuwanci ne a tsakanin kasashen biyu.

A jawabin da ya gabatar a Kamchatka na kasar Rasha a yau Juma'a: Fira ministan Rasha Dmitry Medvedev ya gargadi kasar Amurka da cewa: Sake kakaba wasu sabbin takunkumi kan kasarsa musamman dangane da zargin Rasha da hannu a aiwatar da kisan gilla kan tsohon jami'in leken asirinta a kasar Birtaniya lamari ne da ke matsayin shelanta yakin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Medvedev ya kara da cewa: Kakaba takunkumin Amurka kan harkokin bankin kasar Rasha ko kudaden kasar yana matsayin shelanta yaki ne kan Rasha lamarin da zai fuskanci maida martani a fuskar kasuwanci ko siyasa ko kuma duk wata kafa da zata cutar da kasar Amurka a matsayin maida da martani.Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky