Rabin al’ummar duniya na rayuwa kan kasa da Dala 5

Rabin al’ummar duniya na rayuwa kan kasa da Dala 5

Bankin Duniya yace duk da nasarar da aka samu wajen rage tsananin talauci, har yanzu rabin al’ummar duniya suna rayuwa akan kasa da Dala 5 da Centi 50 a kowacce rana.

Rahoton, wanda Bankin Duniyar ke wallafawa duk bayan watanni shida, ya ce matakan da ake dauka na bunkasa tattalin arzikin kasashe, tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015, yasa an samu raguwar matalauta sama da miliyan 68, adadin mutanen da ya kai na kasar Thailand ko kuma Birtaniya.

Bankin yace sakamakon habakar tattalin arzikin China kuwa, an samu raguwar kashi 35 na matalauta a Gabashin Asia, yayin da talauci ke cigaba da yiwa Yankin Afirka dake kudu da Sahara katutu.

Sai dai a cewar rahoton bankin duniyar, zai wahala a cimma burin rage yawan matalauta a duniya zuwa kasa kashi 3 cikin dari a shekarar 2030, idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin kasashe da dama ke tafiyar hawainiya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky