Qatar Ta Musanta Yin Shisshigi A Cikin Lamuran Kasashen Yankin

Qatar Ta Musanta Yin Shisshigi A Cikin Lamuran Kasashen Yankin

Gwamnatin kasar Qatar Ta Musanta Zargin Wasu Kasashen Larabawa Na cewa tana shisshigi cikin lamaran wasu kasashe a yankin ko kuma tana goyon bayan yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministar harkokin wajen kasar Qatar tana fadar haka a safiyar yau Litinin, ta kuma kara da cewa duk zargin kasashen Saudia, Emarate, Masar da kuma Bahrain suka mata zunzurutun kaayi ne kuma yaki ne da ita don sabanin da suke da ita a cikin wasu lamura a yankin.

Ma'aikatar da kara da cewa kasar zata ci gaba da aiki tare da kuma mutunta dukkan yerjeniyoyi da suka cimma tsakaninta da kasar yankin Tekun farisa. Sannan zata ci gaba da mutunta 'yencin sauran kasashen yankin.

A jiya Lahadi ne wasu kasashen Larabawa wadanda suka hada da Saudia, Masar, Emmarate da kuma Bahrain suka katsae huldan jakadanci da kasar Qatar, suka dakatar da ziraga zirgan jiragen sama, ruwa da na kasa tsakaninsu da ita,  tare da zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky