Osinbajo ya ba da umarnin a yi wa SARS garambawul

Osinbajo ya ba da umarnin a yi wa SARS garambawul

Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayar da umarnin yin garam bawul wa hukumar gudanarwa da kuma ayyukan rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami (SARS).

Mukaddashin shugaban Najeriyar ya ba da umarnin ne bayan korafe-korafen take hakkin bila Adama da aka yi wa rundunar yaki da fashi da makami (SARS) din.

Cikin 'yan kwanakin nan dai matasa a Najeriya sun yi ta neman a soke rundunar a shafukan sada zumunta, musamman ma Twitter ta hanyar amfani da maudu'in #EndSARS .

Wata sanarwa da babban mai taimakawa na musamman na mukaddashin shugaban kasar kan harkar watsa labarai, Laoulu Akande ya fitar, ta ce duk wata rundunar da za ta fito bayan garam bawul din za ta mayar da hankali ne kawai kan aiki da bayanan sirri da hanawa tare da gano fashi da makami da satar mutane, gami da kama wadanda da suka yi irin wadannan laifukan.

Hakazalika Osinbajo ya umarci sufeto janar na 'yan sanda ya tabbatar da cewar dukkan jami'an da za su kasance cikin sabuwar rundunar su zama masu gudanar da ayyukansu ta hanyar mutunta dokakin kasa da kuma kiyaye hakkin bil Adama na wadanda ake zargi da aikata laifi.

Mukaddashin shugaban kasar ya kuma ce dole ne jami'an rundunar su ringa tafiya da alamar rundunar a duk lokacin da suke bakin aiki.Har wa yau, Osinbajo ya umarci shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya da ya samar da wani kwamiti na musamman wanda zai yi bincike game da zargin da ake yi wa rundanr SARS na yin wasu ayyuka ba bisa doka ba, domin mutane su samu damar gabatar da koke-kokensu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky