Nuri Maliki: Iraqi Ba Zata Amince Da Kafa Kasar Kurdawa ba

Nuri Maliki: Iraqi Ba Zata Amince Da Kafa Kasar Kurdawa ba

Tashar Television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Nuri Al-Malili yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacin ganawarsa da Douglas Silliman jakadan kasar Amurka a Bagdaza.

Tashar Television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Nuri Al-Malili yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacin ganawarsa da Douglas Silliman jakadan kasar Amurka a Bagdaza. 

Maliki ya kara da cewa shiye -shiyen da yankin kurdawa na kasar Iraqi yake yi na gudanar da zaben raba gardama na bellewa daga kasar Iraqi tamkar samar da kasar Israila ta biyu ce a yankin gabas ta tsakiya, musamman ma ganin cewa HKI ce kadai a duniya  ta bayyana goyon bayanta ga shirin zaben.

Nuri Al-Maliki ya bayyana haka ne kwanaki biyu bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar rashin amincewa da zaben raba gardaman da kuma bellewar yankin daga kasar Iraqi. Majalisar dokokin yankin  Kurdistan a birnin Arbil dai ta tsada ranar 25 ga wannan watan da muke ciki don gudanar da zaben raba gardaman. 

Banda haka kasashen da suke makwabtaka da yankin na Kurdistan wadanda suka hada da Iran, Syria da kuma Turkiyya duk sun nuna rashin amincewarsu da zaben raba gardamar.288

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky