Nijer : Taron Kasa Da Kasa Na Yaki Da Masu Safarar Bakin Haure

Nijer : Taron Kasa Da Kasa Na Yaki Da Masu Safarar Bakin Haure

Hukumomin wasu kasashen Afirka da na Turai sun gudanar da taron yaki da masu safarar bakin haure zuwa kasashen Turai a Yamai babban birnin jamhoriyar Nijer

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Mohammad Bazoum ministan cikin gida na kasar Nijer yayin bude taron da ya gudana a jiya juma'a na cewa aiki tare a tsakanin kasashen yankin zai fi tasiri wajen yaki da masu safarar bakin haure daga Afirka zuwa Turai, a maimakon ko wata kasa ta yi gaban kanta.

Taron yaki da masu safarar bakin hauren ya samu halartar Jean Yves Le Drian ministan harakokin wajen kasar Faransa da ministocin kasashen ,Senegal, Mali, Mauritania, Chadi, Burkina Faso, Ivory Coast, Guinea, Libya, Jamus, da kuma Italia.

Kafin wannan taro dai, ministan cikin gidan Faransa Gérard Collomb­ ya bukaci  mahalarta taron su dauki kwararen matakai na hana kwararan bakin haure zuwa kasashen na  Turai.

Kasar Nijar dai na a matsayin wata babbar matattara da masu safarar ke amfani da ita don shigar da bakin zuwa kasashen Arewacin Afirka a hanyarsu ta zuwa Turai


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky