Nasrullah: Dakarun Lebanon, Syria Gami Da Hizbullah Suna Samun Nasara A Kan ISIS

Nasrullah: Dakarun Lebanon, Syria Gami Da Hizbullah Suna Samun Nasara A Kan ISIS

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan nasrullah ya bayyana cewa, a ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan ISIS da dukkanin bangarori na dakarun Lebanon, da kuma sojojin Syria tare da mayakan Hizbullah ke yi, ana samun gagarumar nasara.

Tashar talabijin ta almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a daren jiya, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu tun bayan fara kaddamar da farmaki na hadin gwiwa tsakanin sojojin Syria da mayakan Hizbullah a yankunan da ke iyakar Syria da Lebanon, an samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan takfiriyya na Deash.

Sayyid Nasrullah ya kara da cewa, akwai kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin dakarun Lebanon da na Syria da kuma Hizbullah wajen kaddamar da wannan farmaki, inda dakarun Lebanon suke gudanar da nasu a ikin a cikin yankunan Arsal, yayin da sojojin Syria da dakarun Hizbullah suke mayar da hankali a gundumar Qalamun ta yamma.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, a daidai lokacin da ake fatattakar 'yan ta'addan, ana bin salon da aka yi amfani da shi wajen fitar da 'yan ta'addan jabhat Nusra daga yankunan da ta kame a lokutan baya a cikin Lebanon.

A karshen jawabin nasa Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, 'yan ta'addan Daesh sun yi rauni matuka, kuma za a kawo karshenta da izinin Allah.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky