Najeriya za ta ceto daliban Dapchi ta hanyar lalama

Najeriya za ta ceto daliban Dapchi ta hanyar lalama

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da ke ganawa da Sakataren Wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce gwamnatinsa ta zabi ci gaba da tattaunawa a maimakon amfani da karfi domin kubutar da daliban makatarantar Dapchi da sauran dalilan Chibok da ke hannun Boko Haram.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya sanya wa hannu ta ce, babbar fatan gwamnati shi ne ceto ‘yan matan da rayukansu.

Shugaba Buhari ya ce, Najeriya na aiki cikin wata yarjejeniya da kungiyoyin kasashen ketare da masu sulhu don ganin an ceto ‘yan matan ba tare da cutar da su ba.

Shugaban ya kuma mika godiya ga Amurka bisa tallafinta na yaki da ta’addanci a Najeriya, yayin da kuma ya jinjina wa dakarun kasar da ya ce, suna bukatar karin samun horo da kayayyakin aiki.

Kungiyar Boko Haram ta sace daliban makarantar Dapchi da ke jihar Yobe bayan wani farmami da ta kai a cikin wtan jiya, kuma hakan na na zuwa ne bayan shekaru hudu da kungiyar ta sace ‘yan matan Chibok a jihar Borno.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky