Najeriya Ta Cika Shekaru 58 Da Samun 'Yancin Kai

Najeriya Ta Cika Shekaru 58 Da Samun 'Yancin Kai

Yau Nijeriya ke bikin cika shekaru 58 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Britaniya.

Najeriya ta samu yancin kai ne a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 1960.

Bayan karbar ragamar tafiyar da kasar, a matsayin Firaminista, Sir Abubakar Tafawa Balewa, a lokacin ya bayyana cewar, "Kalamai basu iya bayyana farinciki na da annashuwa ba a wannan rana, yau Najeriya ta zama 'yancacciyar kasa mai cin gashin kanta kamar takwarorinta a duniya."  

Bikin na bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da manyan zabukanta a shekara mai zuwa inda yanzu haka manyan jam'iyyun kasar da suka hada da APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke gudanar da zaben fidda 'yan takararsu a zaben gwamnoni.

Tuni dai jam'iyyar APC mai mulki ta tsaida shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta a zaben na badi idan Allah ya kai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky