Najeriya : Mutane 4 Sun Mutu A Arangama Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Shi'a A Kaduna

Najeriya : Mutane 4 Sun Mutu A Arangama Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Shi'a A Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya, na cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu, ciki har da wani dan sanda a wata arangama tsakanin 'yan sanda da almajiran Sheih Ibarhim Al'zakzaky.

Shafin yanar gizo na saharareporters ya rawaito cewa arangamar ta barke a yayin gabatar da Sheikh Ibrahim Yakubu Al'zakzaky gaban kotun ta kaduna a yau Alhamis.

Bayanai sun ce kotun ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa Al'Zakzaky bayan rashin halartar alkali da ke sauraron shari’ar.

A cikin watannin bayan nan dai Jahar kaduna ta zama inda mambobin harkar musuluncin suke yin Zanga-zangar neman sakin Sheikh El-Zakzaky baya ga babban birnin tarayya Abuja.

Tun a cikin watan Disamba na 2015 ne aka kama Sheikh El-Zakzaky tare da mai dakinsa Zeinat bayan harin da sojojin kasar suka kai a gidansa, biyo wani rikici tsakanin 'yan shi'ar a garin Zaria da sojojin.

Magoya bayan Zakzakin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi dubu guda, ciki har da 'ya 'yansa, sannan aka yi awangaba da wasu da dama.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky