Najeriya: APC Ta Lashe Zaben Gwamna A Jahar Osun

Najeriya: APC Ta Lashe Zaben Gwamna A Jahar Osun

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayyana Gboyega Oyetola, na jami’yyar APC mai mulki, a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Osun.

A jiya Alhamis aka kada kuri’un zaben kujerar gwamnan da suka rage a wasu rumfunan zabe guda bakwai, wadanda suke kananan hukumomi hudu na jihar ta Osun, saboda dakatar da kada kuri’un, a ranar Asabar din da ta gabata, bisa wasu dalilai da suka hada da na tsaro da kuma sahihanci.

Kananan hukumomin da aka gudanar da cikon zaben kujerar gwamnan sun hada da, Ife ta Arewa, Ife ta Kudu, Kajola da kuma Osogbo.

Yayin sanar da sakamakon, kwamishinan hukumar zaben jihar ta Osun, Farfesa Joseph Fuwape, ya ce Oyetola na jam’iyyar APC, ya lashe zaben gwamnan da kuri’u dubu 255,505, yayinda Adeleke dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’u 255,023.

Sai dai tuni jam’iyyar adawa ta PDP, da kuma gamayyar jam’iyyun da suke goyon bayanta suka yi watsi da sakamakon, wanda suka ce babu gaskiya a cikinsa, dan haka za su kalubalanci sakamakon zaben  a kotu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky