Musulmi Mahajjata Fiye Da Miliyon Biyu Ne Suka Fara Aikin hajji A Mina

Musulmi Mahajjata Fiye Da Miliyon Biyu Ne Suka Fara Aikin hajji A Mina

A jiya laraba ne maniyyata hajjin bana fiye da miliyon biyu ne suka kwarara daga Makka zuwa mina don raya ranar tarwiya da kuma fara aikin hajjin bana,

Jaridar Araba news ta kasar saudia ya bayyana cewa mahajjata sun fara aikin hajjin a jiya, kuma jami'an tsaro suna taimakawa yansanda hanya don tabbatar da cewa babu wata matsala sanadiyyar cinkoson mutane. 

A safiyar yau Alhamis ne mahajjatan zasu tsaya a filin mina kusa da dutsen Jabal Rahama inda zasu yi yi suna addu'o'i da kuma tawaliu ga ubangiji har zuwa magarima a lokacinda zasu kwarara zuwa mash'aril Haram inda zasu bada sallolin magariba da issha. Sai kuma gobe salla mahajjatan zasu fara jifan shaidan. 

A bangaren kiwon lafiya kuma hukumomin sun ajiye ma'aikatan bada agajin gaggawa na Hilal Ahmar a ko wani lungu da sako da mani da kuma arafa don bada taimakon gaggawa a duk lokacinda wata matsala ta taso.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky