Morsi Ya Ce Ba Zai Taba Amincewa Da Juyin Mulkin Da Sisi Yayi Masa Ba

Morsi Ya Ce Ba Zai Taba Amincewa Da Juyin Mulkin Da Sisi Yayi Masa Ba

Hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi ya bayyana cewar ba zai taba amincewa da juyin mulkin da shugaban kasar Masar din na yanzu Abdel Fattah al-Sisi yayi masa.

Kafar watsa labaran Arabi21 da ke birnin London ne ta bayyana hakan inda ta jiyo dan hambararren shugaba Morsi, Abdullah Morsin yana fadin hakan inda ya ce mahaifin na su ya sanar da su cewa ba zai taba amincewa da juyin mulkin da aka yi masa ba, yana mai cewa yayi hakan ne don girmama zabin da mutanen Masar suka yi masa a matsayin shugaban kasa.

Abdullah Morsi ya bayyana cewa mahaifin na su ya bayyana musu hakan ne a ganawar da suka yi da shi a inda ake tsare da shi, wanda hakan ita ce ganawa ta uku da aka bar su suka yi da shi tun daga lokacin da aka kama da kuma tsare shi a shekara ta 2013.

Hambararren shugaba Morsin dai yana fuskantar hukumcin kisa da sauran hukunce-hukunce na dauri a gidan maza da wasu kotuna suka yanke masa saboda zargin da ake masa na tada fitina, barazana ga tsaron kasa da kuma gudanar da ayyukan leken asiri don amfani 'yan kasashen waje.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky