Ministar Kudi A Nigeria Ta Ajiye Aikinta

Ministar Kudi A Nigeria Ta Ajiye Aikinta

Ministar kudi a Najeriya Kemi Adeosun ta yi murabus daga kan mukaminta bayan samunta da takardun jabu na yi ya wa kasa hidima.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ta dauka na yin murabus daga kan mukamin nata.

Kemi Adeosun ta ce ta yi murabus ne domin kare mutuncin gwamnatin Najeriya, sakamakon batun da ake yi na takardunta da hidimar kasa marassa inganci.

Tun a cikin watan Yulin da ya gabata ne jaridar Premium Times ta bayar da wani rahoto da ke nuna cewa takardun yi wa kasa hidima da ministar kudin ta Najeriya ta bayar na bogi ne, wanda hakan ya jawo wa gwamnatin Buhari suka, amma duk da haka dai ta ci gaba da rike mukaminta har zuwa jiya Juma'a da ta yi murabus.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky