Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Maida Martani Kan Takwaransa Na Kasar Amurka

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Maida Martani Kan Takwaransa Na Kasar Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya maida martani kan furucin karya da takwaransa na kasar Amurka ya yi kan kasar Yamen domin kare bakar siyasar Saudiyya kan matakan wuce gona da iri da take dauka kan kasar ta Yamen.

A martanin da ya mayar a yammacin jiya Alhamis kan furucin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo dangane da kasar Yamen cewar mahukuntan Saudiyya sun gabatar da taimakon miliyoyin dalolin Amurka domin jin kan bil-Adama a Yamen tare da kokarin ganin kasar bata rushe ba; Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya tambayi Mike Pompeo cewa: Shin baya jin kunyar shirga mummunar karya irin wannan a rayuwarsa?

Muhammad Jawad Zarif a shifinsa na Twitter ya rubuta cewa: Shin Mike Pompeo yana bukatar ganin al'ummar Yamen sun zuba ido ne ana ta yin luguden wuta kansu domin halaka su ko rusa gidajensu da cibiyoyi da ma'aikatu da masana'antu gami da makarantu, ba tare da sun dauki matakin kare kai daga irin wadannan matakan wuce gona da iri ba? Shin irin wannnan miliyoyin dalar Amurka da Saudiyya take kashewa a yakin da ta kaddamar kan kasar ta Yamen amfanin al'ummar Yamen ne?

Jawad Zarif ya kara da jaddada cewa: Hakika akwai bukatar Mike Pompeo ya ji kunyar furta irin wannan mummunar karya da al'ummun duniya suke da masaniya kan hakikanin abin da ke gudana a kasar ta Yamen.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky